An tuhumi dan bindiga a Amurka da kisa ba da nufi ba

George Zimmermann
Image caption George Zimmermann

An tuhumi mutumin da ya bindige wani matashi bakar fata har lahira a jihar Florida na kasar Amurka da laifin aikata kisa ba da manufa ba.

An sake kama George Zimmermann ne dan shekaru 28 a duniya bayan zanga zanga da kiraye kiraye ga sashen shariar kasar.

To sai dai masu gabatar da kara a jihar Florida sun ce matsin lamba da mutane ke nunawa ba shi ne ya yi tasiri akan matakin da suka dauka ba.

George Zimmerman wanda mai sa ido ne a unguwanni, na sa kai, ya yi ikirarin cewa ya halaka matashin ne dan shekaru 17 a duniya wato Trayvon Martin don kare kansa, wanda a karkashin dokar jihar Florida ba laifi ba ne.