An yi gangamin nuna goyon baya a Koriya ta Arewa

Gangami a Koriya ta Arewa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gangami a Koriya ta Arewa

Dubun dubatar 'yan kasar Korea ta Arewa ne suka halarci wani gangami domin yaba wa iyalan dake mulkin kasarsu, sa'o'i kadan bayan da wani yunkuri na harba tauraron dan Adam da aka dade ana yayatawa ya ci tura.

Shugaban kasar Koriya ta Arewan , Kim Jong-un ne ya jagoranci bikin a birnin Pyongyang.

Korea ta Arewa ta amince cewa, ba ta yi nasara ba wajen kaddamar da wannan tauraron dan adam, wanda ya tarwatse jim kadan bayan harba shi.

Sai dai duk da koma bayan da Korea ta arewan ta fuskanta, kasashe sun koka da cewa, a zahiri Korean tana gwada fasahar kera makami mai linzami ne, wanda hakan ya saba wa kudurorin kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya.

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon, ya bayyana matakin a matsayin abinda bai dace ba.

Karin bayani