Cin hanci ya dabaibaye binciken fansho a Nigeria

Zargin bayar da hanci ya kaure tsakanin kwamitin Majalisar Dattawan Nigeria dake binciken yadda ake kashe kudaden fansho da shugaban kwamitin musamman da gwamnatin kasar ta kafa don yin garambawul a harkar fashon.

Wasu mambobin kwamitin sun zargi shugaban kwamitin musamman da gwamnatin kasar ta kafa a harkar fashon Abdurrashid Maina da yunkurin ba su cin hanci.

To, amma a na sa bangaren, Abdurrashid Maina ya ce shafa masa kashin kaji kawai ake neman yi.

Shugaban kungiyar CISLAC mai sa ido kan harkokin majalisa a Nigeria Auwal Musa Rafsanjani ya ce kamata ya yi a rushe kwamitin, don a cewar sa babu alamun mambobin kwamitin za su yi gaskiya a binciken.

Karin bayani