Sojoji da 'yan siyasa na ganawa a Guinea Bissau

Jam'iyyun adawa a kasar Guinea Bissau da ke yammacin Afirka na ganawa da sojojin da suka kwaci mulki a ranar Alhamis din da ta wuce.

Sojojin sun ce suna shirin mayar da kasar bisa turbar demokradiyya.

Tsohuwar jam'iyya mai mulki bata shiga shawarwarin ba.

Kuma har yanzu ba a ji duriyar dan takararta, a zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa nan gaba a cikin wannan watan ba, watau Carlos Gomes Junior.

A cewar sojojin, yana nan kalau amma tsare.

Kasashen duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin na Guinea-Bissau.

Karin bayani