An kai munanan hare-hare a Afghanistan

An kai munanan hare-hare a Afghanistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ofishin jakadancin Burtaniya na cikin wuraren da aka hara

'Yan bindiga sun kaddamar da hare-hare kan wurare da dama a Kabul babban birnin kasar Afghanistan da wasu biranen kasar, ciki har da ofishin jakadancin Burtaniya.

Mai magana da yawun kungiyar Taliban ya ce mahara sun kai hari kan yankin da jami'an diflomasiyya ke zaune da hedkwatar kungiyar tsaro ta Nato da kuma ginin Majalisar dokokin kasar.

An kuma ji karar fashewar wasu abubuwa a sassa daban-daban na birnin Kabul.

Mai magan da yawun Taliban ya kuma ce an kai wasu hare-haren a gundumomin Logar da Paktia.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa an kai harin kunar bakin wake a birnin Jalalabad.

Nato ta ce ta samu labarin kai hare-hare a wurare bakwai a Kabul, amma kawo yanzu bata samu labarin ainahin barnar da harin ya haifar ba.

Hayaki na tashi

Ofishin jakadancin Burtaniya na cikin wuraren da aka hara, inda aka harba makaman roka biyu kan katangar ginin.

An kuma harba roka kan wani gida da jami'an diflomasiyyar Burtaniya ke amfani da shi, kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

An ji karar fashewar abubuwa akalla bakwai a tsakiyar birnin Kabul yayin da ake ta harbe-harbe a unguwannin da jami'an diflomasiyyar kasashen Yamma ke zaune.

Rahotanni sun ce mazauna birnin na tserewa domin neman mafaka, yayin da ake ta jin karar jiniya a yankin Wazir Akbar Khan.

An ji karar fashewar wasu abubuwa a kusa da ginin Majalisar dokokin kasar da ke yammacin Kabul, kuma 'yan sanda sun ce an kaiwa ginin hari.

Karin bayani