Okonjo-Iweala na samun goyon baya

Hakkin mallakar hoto AFP

Yayin da darektocin Bankin Duniya ke shirin zaben shugaban bankin 'yar takarar Najeriya a mukamin, ta kara samun goyon baya.

Shugabar hukumar da ke kula da kasuwanin hannayen jari ta kasar, Arunma Oteh, ta ce Okonjo-Iweala ita ce ta fi dacewa da mukamin, ganin yadda ta kwashe shekaru da dama a bankin duniyar, da kuma matsayinta na ministar kudin Najeriyar.

Tana takara ne da mutumen da shugaba Obama ke marawa baya, watau malamin jami'ar nan Ba-Amirke, Jim Yong Kim, wanda shine ake ganin zai kai labari.

A karkashin wata yarjajeniya, a kodayaushe Ba-Amurke ne ke shugabancin Bankin Duniyar, yayin da shi kuma shugaban asusun bada lamunin IMF ke fitowa daga nahiyar Turai.