Breivik ya gurfana a gaban alkali

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Anders Behring Breivik mutumin da ake zargi da kisan mutane saba'in da bakwai a Norway cikin watan Yulin da ya gabata ya musanta aikata laifin, yayin soma shari'arsa a yau.

Anders Behring Breivik ya amsa kai harin, amma ya musanta cewa, shi ke da laifi, yana mai cewa, ya kai harin ne da nufin kare kai.

Breivik ya gurfana ne a gaban kotu sanye da bakar riga kuma bai nuna wata nadama ba a lokacinda mai gabatar da kara ya yi bayanin yadda wadanda da Breivik din ya harba suka mutu.

Breivik ya shaidawa kotu cewa ya kashe mutanen ne don kare Norway daga musulunci da kuma bakin al'ummu.

Ana saran za a yi makonni goma ana shara'ar