Mambobin majalisar dinkin duniya sun isa Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Syria

Mambobin majalisar dinkin duniya da za suyi aikin sa ido a Syria sun isa babban birnin Kasar na Damascus.

Wani mai magana da yawun majalisar dinkin duniya ya fadawa BBC cewar, mambobin majalisar dinkin duniyar su shida, zasu soma ganawa da gwamnati tare da 'yan adawa, kafin daga bisani su shiga cikin gari.

Za a kara yawansu, zuwa mutum talatin nan da wasu 'yan kawanki masu zuwa

Ana dai cigaba da samun tashin hankali a Syrian, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wutar data soma aiki tun ranar alhamis.

An dai bada rahotan barkewar fada tsakanin dakarun gwamnati da kuma 'yan tawaye a garin Homs na Syrian.

Daya daga cikin masu fafutuka a Syrian, yace mutane sha- hudu sun mutu

Karin bayani