'Yan makaranta a Afghanistan sun ci guba

Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan

An kwashi yara mata 'yan makaranta fiye da dari a arewa maso gabashin Afghanistan zuwa asibiti saboda wani abin da suka ci wanda ake zargin yana dauke da guba—bayan sun koka cewa suna jin kasalar jiki da ciwon kai da jiri.

Daraktan lafiya na lardin Takhar ya ce ’yan matan sun fada wannan yanayi ne bayan sun sha wani ruwa wanda ke bulbula a cikin makarantarsu a kauyen Rustaq.

Wani jami'in hukumar ilimi a Kabul ya ce binciken share-fagen da aka gudanar ya nuna cewa an sanya guba ne a cikin ruwan.

Wani jami'i a yankin na Takhar ya bayyana cewa yana kyautata zaton wadanda ba sa goyon bayan zuwan ’yan mata makarantar boko ne suka sanya gubar a cikin ruwan.

Karin bayani