Spain ta yi Allah wadai da matsayar Argentina

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption masu neman aiki a Spain

Gwamnatin Spain tayi allawadai da abinda ta kira wata sanarwa mai tsauri da Kasar Argentina ta fitar, game da shirinta na maida wani kamfanin mai da Kasar Spain din ke gudanarwa a Kasar mallakar gwamnati.

Wakilin BBC yace, ministan harkokin wajen Kasar Spain, ya fadawa manema labaru cewa, matakin da Argentinan ta dauka ya lalata abokantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugabar Argentinan Cristina Fernandez dai, tace tana bukatar gwamnatin Kasar ta mallaki kashi hamsin da daya cikin dari na hannun jarin kamfanin mai suna YPF, wanda wani kamfanin Kasar Spain ya kawo cikin Argentinan fiye da shekaru goma da suka gabata, karkashin wani shiri na saida hannun jari

Karin bayani