Tarayyar Turai za ta dauki mataki a kan Argentina

Shugabar Argentina Cristina Kirchner Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabar Argentina Cristina Kirchner

Tarayyar Turai ta ce, tana duba yiwuwar daukar duk matakin da ya dace a kan Argentina, wadda tace zata kwace wani kamfani na 'yan Spain, domin maida shi mallakar gwamnati.

Matakin kwace kamfanin da shugaba Cristina Fernandez ke shirin dauka, ya biyo bayan takaddamar da aka yi tsakanin Argentina da Birtaniya, akan batun hakar mai a gabar tsibirin Falkland.

Wakilin BBC ya ce, 'yan adawa a Argentina suna fargabar cewa, kwace kamfanin man mallakar 'yan Spain, zai kawo koma baya ga zuba jari a kasar.

Tuni dai shugabar Argentinar tayi watsi da duk wata barazana akan matakin da ta dauka.

Karin bayani