Kim ya ce zai mai da hankali kan tattalin arzuki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kim

Mutumin da aka zaba a matsayin shugaban bankin duniya na gaba, yace babban abinda zai maida hankali akai, shine bunkasa tattalin arziki, domin samar da ayyukan yi da kuma fitar da mutane daga cikin kangin talauci.

A wata hira da BBC, Jim Yong Kim yace abune wanda ba za a amince da shi ba kwata kwata, cewa mutane biliyan guda na rayuwa cikin tsananin talauci.

Bankin duniyar dai ya bi al'adar nan ta zaben Ba'amurke a matsayin wanda zai Shugabanci bankin.

Amma sai dai nadin nasa, na zuwa ne bayan da Ministar Kudi ta Najeriya Ngozi Okonja Iweala ta kalubalance shi.

Shima dai kwararre ne kan batutuwan da suka shafi lafiya a Kasashe masu tasowa, kuma yace Kasashe masu Tasowar, nada babbar murya a bankin duniyar.

Karin bayani