Sojin Bissau sun amince su maida mulki ga farar hula

Carlos Gomes Junior, tsohon praministan Guinea Bissau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Carlos Gomes Junior, tsohon praministan Guinea Biiasu

Wata tawagar wakilan kungiyar kasashen Afrika ta Yamma da ta gana da hukumomin sojin da suka kwace mulki a kasar Guinea Bissau ta ce sojojin sun amince su mayar da mulki ga hannun farar hula, da kuma dawo da aiki da kundin tsarin mulki.

Hakan ya biyo bayan ganawar da suka yi ne a Bissau, babban birnin kasar.

Ranar Alhamis din makon jiya ne sojojin suka kwace mulki, suka kama shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar, tare da tsohon praministan kasar, wanda ke takara a zagaye na biyu na zaben da ya kamata a gudanar karshen wata nan.

A waje daya kuma kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bada sanarwar dakatar da kasar ta Guinea Bissau, tana mai cewar har sai an dawo da bin kundin tsarin mulki.