Chelsea sun fi mu dama - Pep Guardiola

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona ce mai rike da kanbun na zakarun Turai

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya ce a yanzu Chelsea ta fi su damar tsallake wa zuwa wasan karshe na gasar zakarun Turai bayan da suka doke Barca a wasan farko a Stamford Bridge.

"Ina gani su ne a kan gaba saboda samun nasara da ci 1-0 a gida ba karamar dama bace a gare su," a cewar Guardiola bayan wasan da aka fafata ranar Laraba.

Sai dai takwaransa na Chelsea Roberto di Matteo ya nace cewa har yanzu wasan a bude yake - kowa zai iya samun nasara.

"Ba na ganin wannan nasarar ta dora mu a samansu," a cewar Di Matteo. "Kowacce kungiya na da damar tsallakewa kamar 'yar uwarta."

Didier Drogba ne ya zira wa Chelsea kwallon da ta samu daf da za a tafi hutun rabin lokaci, abinda ya basu damar tafiya Nou Camp ranar Talata domin zagaye na biyu da kwarin gwiwa.

Chelsea ta samu wannan nasara ce duk da cewa Barcelona ta mamaye kusan baki dayan wasan.

Kafin nasarar da tawagar ta sa ta samu, Di Matteo ya nanata cewar wajibi ne su dage idan har suna son kaiwa wasan karshe a karo na biyu a tarihinsu.

Karin bayani