Anders Breivik zai bada shaida ga kotu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Breivik

A yau ake tsammanin mai tautsauran ra'ayin nan dan Kasar Norway Anders Breivik, zai sake bada shaida a gaban kotu a rana ta biyu.

Za a tambayi Breivik yayi bayanin dalilin da yasa ya hallaka mutane saba'in da bakwai a wasu hare- hare guda biyu, a ciki da kuma wuraren babban birnin Kasar na Oslo a watan Julin bara.

Wakilin BBC yace a zaman kotun jiya litinin, Breivik ya amince da sanya bam a cikin wata mota, da kuma bude wuta kan wani sansanin matasa a tsibirin Utoya.

Amma ya ki amincewa da cewar ya aikata wani mugun laifi, yana mai cewa yayi hakanne domin ya kare kansa daga tarun al'adun Kasar da kuma addinin musulunci.

Ba a tsammanin shari'ar zata wuce makonni goma.

Karin bayani