Sudan ta yi barazanar ci gaba da hari kan Sudan ta Kudu

sojojin Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto sudansouth
Image caption sojojin Sudan ta Kudu

Gwamnatin kasar Sudan ta ce za ta ci gaba da kai hari kan Sudan ta Kudu har sai ta janye daga yankin Heglig, dake da arzikin man fetur.

Jakadan Sudan a Kenya, Kamal Isma'il Saeed ya ce kasarsa zata yi amfani da duk wata hanyar da take da ita wajen sake kwace iko da yankin.

A ranar litinin ne majalisar dokokin Sudan din ta bayyana Sudan ta Kudu a matsayin abokiyar gabarta ta kuma yi kira da a sake kwace Heglig, yankin da ke da matukar muhimmanci.