Tsohon shugaban kasar Mali ya tafi Senegal

Amadou Toumani Toure Hakkin mallakar hoto
Image caption Hambararren Shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Toure

Rahotanni daga Senegal sun ce hambararren Shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Toure, ya fice daga kasarsa, ya shiga jirgin sama zuwa birnin Dakar.

Tun farkon makon nan kasar ta Senegal ta bayar da labarin cewa Mista Toure, wanda sojoji suka hambarar a watan jiya, ya nemi mafaka ne a ofishin jakadancinta da ke Bamako, babban birnin kasar ta Mali.

A halin da ake ciki kuma sojoji a kasar ta Mali sun saki mutanen nan ashirin da biyu wadanda suka hada da sojoji da 'yan siyasa—akasarinsu aminan Mista Toure, wadanda aka tsare farkon makon nan.