Sudan da Sudan ta Kudu na nunawa juna yatsa

Omar al-Bashir

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Omar al-Bashir na Sudan yana cewa zai so ya 'yantar da mutanen Sudan ta Kudu

Kasar Sudan da Sudan ta Kudu suna gab da afkawa yaki gadan-gadan bayanda Shugaba Omar al-Bashir ya furta cewa yana so ya ’yantar da mutanen Sudan ta Kudu daga gwamnatinsu.

Wadannan kalaman da ya yi a wajen wani taron gangami a Khartoum ya biyo bayan kwanakin da aka shafe ne ana gwabza fada a kan iyakokin kasashen biyu—abin da Shugaba al-Bashir ya ce ba za a ci gaba da lamunta ba.

Ya ce ko dai Sudan ta zarce da yakin ne zuwa Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, ko kuma ita Sudanta Kudu ta kora yakin ta dangana da birnin Khartoum na kasarsa.

Ya shaidawa taron cewa za a mayar da martani a kan duk wani hari da Sudan ta Kudu ta kai:

“A yanzu muna gaya musu cewa idan suka cire idon wani za mu cire idonsu, idan aka cire hakorin wani za mu cire nasu, idan aka raunata wani za mu raunata na su”, in ji Shugaba al-Bashir.