Tashin bam ya hallaka mutane a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters

Akalla mutane 35 sun hallaka a Iraki sakamakon wasu jerin hare-haren bama-bamai.

Bama-baman sun tashi ne a Bagadaza da kuma wasu sassan kasar.

Jami'an gwamnatin Irakin sun ce wasu karin mutane 100 sun samu raunika a hare-haren.

Ministan lafiya na Irakin, Majeed Hamad Amin, ya tsallake rijiya da baya yayinda aka kai wa ayarin motocinsa hari, a birnin Bagadaza.

Hakazalika wasu bama-baman sun tashi a biranen Kirkuk da Samarra.

Wakilin BBC a Bagadaza, ya ce yadda aka kai hare-haren a kusan lokaci guda, wata alama ce da ke nuna cewa har yanzu akwai jan aiki a gaban gwamnatin kasar a yakin da take da masu tayar da kayar baya.

Karin bayani