Dimbin 'yan gudun hijira na kara shiga Mauritania daga Mali

'Yan gudun hijirar Mali
Image caption Ana bukatar dauki

Kungiyar agaji ta kasa da kasa, Medecins Sans Frontieres, ta ce an samu matukar karuwar yawan 'yan gudun hijira da ke tsallakawa cikin Mauritania daga Mali, sakamakon rikicin tawayen da ake yi a arewaci kasar.

Kungiyar ta Medecins Sans Frontieres ta ce a cikin makonni biyu da suka wuce, yawan 'yan gudun hijirar ya karu daga dari biyu a rana zuwa dubu daya da dari biyar.

Wakilin BBC ya ce kungiyar ta yi gargadin cewa yanayin da ake ciki a sansanonin 'yan gudun hijirar na kan iyaka da Mauritania mummuna ne, kuma bai kai mizanin da ya dace ba saboda rashin tsabtataccen ruwan sha da mummunan zafi da kuma iskar mai cike da kasa.

Da dama daga cikin 'yan gudun hijirar kuma suna da fama da matsalolin rashin lafiya da suka hada da tamowa, kuma asibiti mafi kusanci da sansaninsu, sai an yi tukin sa'o'i shidda a mota kafin a isa wurin.

Karin bayani