Bom ya subuce daga jirgin yakin Najeriya

Hafsan sojin saman Najeriya da Ministan tsaro
Image caption Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Oluseyi Petinrin, da Ministan Tsaro na kasar, Bello Halliru

Wani bom dake jikin wani jirgin saman yaki na sojin saman Najeriya ya subuce.

Rokar da ke harba bom din dai ta kwace ne yayin da sojojin ke wadansu 'yan aikace-aikace a jikin jirgin saman a sararin samaniya ta barikin mayakan saman dake Jihar Rivers a kudu maso kudancin Nijeriya.

Rundunar sojin ta shaidawa BBC cewa bayan da bom din ya subuce, ya yi gudun fiye da kilomita hudu kafin ya fada kan wani gida a unguwar Woji a birnin Fatakwal.

Ba a dai sami hasarar rayuka ba lokacin da bom din ya fada a kan gidan.