Ba wanda ya tsira a hadarin jirgi a Pakistan

Karikicen jirgin da ya yi hadari a Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Karikicen jirgin da ya yi hadari a Pakistan

Wani jirgin saman fasinja ya fado a kusa da Islamabad, babban birnin kasar Pakistan, ya kuma hallaka mutanen da ke cikinsa su dari da ashirin da bakwai.

Wakilin BBC ya ziyarci asibitin PIMS a birnin na Islamabad, inda motocin daukar marasa lafiya ke jerin gwano suna kai gawarwakin mutanen da suka rasa rayukansu.

Babu wanda ya tsira da ransa a hadarin.

Dangin da dama daga cikin fasinjojin da ke jirgin dai sun yi circirko a kusa da asibitin suna jiran tsammani, amma dai babu wani labari mai dadin ji.

Daya daga cikin dangin fasinjojin da ke jirgin ya bayyana cewa “har yanzu ina jira ko zan samu wani labari, kafin in je in duba ko zan gane mahaifina da ’yar uwata—ko suna raye ko sun mutu, a gaskiya ban sani ba”.

Jirgin, wanda ya taso daga Karachi, ya fada cikin mawuyacin hali ne 'yan mintuna kadan kafin ya sauka.

Kamfanin da ya mallaki jirgin, Bhoja, ya ce rashin kyawun yanayi ne ya haddasa hadarin.

An dai yi ruwa da iska tare da tsawa mai karfin gaske a yankin a lokacin.

Ana ma tsokacin cewa walkiya ce ta bugi jirgin.

Sai dai kuma wadansu mutanen da dama suna diga ayar tambaya a kan tsufan jirgin, da sahihancin na'urorin kiyaye hadurra na Pakistan da ma dalilin da ya sa aka kyale jirgin ya yi yunkurin sauka duk da rashin kyawun yanayi.