Obama ya tsawatarwa Sudan da Sudan ta Kudu

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi kira ga Sudan da Sudan ta Kudu su kawo karshen fadan da suke yi, yana mai cewa kamata ya yi shugabannin kasashen biyu su yi ta-maza su warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi.

Mista Obama ya ce ya kamata Sudan ta dakatar da kai hari a kan makwabciyarta, ita kuma Sudan ta Kudu ta daina mara baya ga ’yan tawayen da ke cikin Sudan.

Tun da farko dai jayayya ta barke tsakanin kasashen biyu dangane da janye sojojin Sudan ta Kudu daga yankin Heglig mai arzikin man fetur wanda ake takaddama a kansa.

Sanarwar da hukumomi a Sudan suka fitar cewa rijiyoyin man da ke yankin na Heglig sun koma karkashin ikonsu ta faranta ran jama'a a kasar ta Sudan.

Sai dai kuma karin bayanin da ma'aikatar tsaron Sudan ta yi—wanda Shugaba Omar al-Bashir ya jaddada—cewa sojojin kasar ta Sudan ne suka fatattaki dakarun Sudan ta Kudu ya jawo martani mai zafi daga ketaren iyakar.

Yayin da yake jawabi a wajen wani gangami, bayan ya yi barazanar ci gaba da hana Sudan ta Kudu amfani da bututan man Sudan don fitar da mai, Shugaba al-Bashir ya yabawa sojojin kasarsa saboda jaruntakar da suka nuna:

“Lokacin da mutanensu suka sha kashi, sojojinmu suka murkushe su baki daya suka kuma yi fafata-fata da su, sai suka ce wai za su janye a cikin kwanaki uku. Daga nan ne Salva Kiir ya umarci dakarunsa su janye”, in ji al-Bashir.

Sai dai kuma Mataimakin Shugaban Kasar Sudan ta Kudu, Riak Machar, ya karyata wadannan kalamai na al-Bashir:

“Abin da Khartoum ke fadi ba gaskiya ba ne—dakarunmu suna nan a Heglig”.

Ya kuma kara da cewa, “Mun amince ne da shawarar gwamnatin Sudan ta Kudu ta janyewa, za kuma mu aiwatar da ita. Na san hukumomi a Khartoum cika baki kawai suke yi, suna zaton sun kori dakarunmu daga Heglig”.

Sai dai kuma Mista Machar ya nuna har yanzu tsgune ba ta kare ba, yana mai cewa janye dakarunta ba ya nufin Sudan ta Kudu ta janye ikirarinta na mallakar yankin na Heglig.

A cewarsa dalilin da ya sa Sudan ke jayayya a kan Heglig daya ne kawai: saboda yankin na da arzikin man fetur.