Kwamitin Sulhu zai kada kuri'a kan Syria

Wadansu daga cikin mambobin Kwamitin Sulhu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wadansu daga cikin mambobin Kwamitin Sulhu

Nan gaba a yau Asabar ake sa ran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a a kan wani daftarin kuduri game da kasar Syria.

Hakan dai zai bayar da damar tura wakilai dari uku masu sa ido a kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Jami'an diflomasiyya sun ce an hada daftarin kudurin ne daga kudurori dabam-dabam na Rasha da Tarayyar Turai.

Za a tura tawagar masu sa idon ne a cikin watanni uku kuma za su kasance a karkashin kariyar sojojin gwamnatin Syria.