An fara zaben shugaban kasa na Faransa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sarkozy da Hollande

An fara gudanar da zaben shugaban Kasar Faransa zagaye na farko inda za'a fafata tsakanin yan takara goma da suka futo neman zaben.

Dokokin zaben Kasar dai sun haramtawa 'yan takara gudanar da kamfe da kuma jin ra'ayoyin jama'a a ranar zabe.

Shugaba mai ci Nicolas Sarkozy dai yana fuskantar kalubale daga dan-gurguzu Francois Hollande, da kuma wasu 'yan takara guda takwas.

zaben na gudana ne a wani lokaci na rashin tabbas game da tattalin arzikin kasar, kuma ana ganin cewar ba za a sami fitowar jama'a sosai ba a zagayen farko na zaben.

Karin bayani