Amurka da Afghanistan sun cimma yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Amurka da Afghanistan sun yi gyare-gyare na karshe akan wani daftarin yarjejeniyar da ke fayyace makomar dangartakar su bayan Amurkar ta janye dakarun ta daga kasar.

A shekarar 2014 ne aka shirya Amurka zata kammala janye dakarun ta a Afghanistan din.

Bayan sun shafe fiye da shekara suna tattaunawa, bangarorin biyu sun rattaba hannu akan daftarin.

Yanzu za a tura shine zuwa majalisar dokokin Amurka da majalisar dokokin Afghanistan domin amincewar su.

Kawo yanzu dai babu wani karin bayanin da aka bayar akan yarjejeniyar

Karin bayani