Gwamnatin Netherlands ta yi murabus

Majalisar zartarwar Netherlands Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Majalisar zartarwar Netherlands

Praministan Netherlands, Mark Rutte, yayi murabus tare da gwamnatinsa, sakamakon takaddamar da ta kunno kai a kasar, game da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Murabus din dai zai share fagen yin zabe a Netherlands din nan gaba cikin wannan shekarar.

Murabus din Praministan dai ya biyo bayan cijewar tattaunawa akan tsuke bakin aljihun gwamnati, tsakanin Mista Rutte da shugaban jam'iyyar Freedom ta masu ra'ayin rikau, Geert Wilders, wanda ya ki amincewa da duk wani mataki na rage kudaden da gwamnati take kashewa.

Shi dai Mista Rutte ya so ne ya zabge Euro biliyan sha shida daga kasafin kudin kasar domin cimma tsarin kasashen Turai na rage gibi a kasafin kudi.

Karin bayani