Ana kiran da a sauke wasu ministoci a Najeriya

Masu zanga zanga a Najeriya Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu zanga zanga a Najeriya

A Nigeria, kungiyar United Action for Democracy ta gudanar da wani kwarya kwaryan gangami a sassan kasar da dama.

Kungiyar ta kira wannan gangamin ne da nufin fadakar da jama'a game da abin da ta kira, irin yadda wasu 'yan tsiraru ke wawure dukiyar kasa, tana mai kira ga gwamnatin Nigeria da ta kori wasu ministoci ukku.

Tun bayan da kwamitin majalisar wakilan Nigeria da ya gudanar da bincike kan kudaden tallafin man fetur ya fitar da rahotonsa a makon jiya, yana mai zargin ana aikata ba daidai ba, wasu ke kiran da a dauki mataki kan duk wadanda aka samu da laifi.

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanoni biyu dake gudanar da bincike kan kudaden rarar man na gwamnati.

Karin bayani