Sabon rigakafin cututukan kananan yara a Najeriya

Rigakafi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rigakafi

A Najeriya, hukumar da ke kula da lafiya a matakin farko, ta gabatar da sabon maganin rigakafin wasu cututtuka biyar da ke addabar kananan yara.

Cututtukan dai sun hada da makarau, da tarin shika, da sarke hakora, da ciwon hanta da kuma sankarau.

A cewar hukumar, maganin rigakafin zai saukakawa iyayen yara wahalhalun da suke fuskanta wajen neman magungunan rigakafin wadannan cututtuka, tun da an hade magungunan wuri guda.

Karin bayani