Sudan ta ce ba batun sasantawa da Sudan ta Kudu

Dakarun SPLA a garin Bentiu Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun SPLA a garin Bentiu

Wani jirgin saman yakin Sudan ya kai hare haren bam a Sudan ta Kudu, kwana guda bayan da Sudan ta Kudun ta janye sojojinta daga yankin da kasashen biyu ke takaddama kansa.

An kashe akalla mutum guda, ankuma raunata wasu da dama a lokacin samamen.

Wani jami'in gwamnatin Sudan ta kudu, Mac Paul yace harin yana da muni sosai, inda kuma ya ce kara dagulewar al'amurra ne.

Yanzu haka dai shugaba Omar Al-Bashir na Sudan ya ce babu wani batun sasantawa da Sudan ta Kudu.

Ranar lahadi ne dai Sudan ta kudu tace ta kammala janyewa da yankin Sudan da ta mamaye.

Karin bayani