Matsin tattalin arziki ya takura 'yan Holland

Image caption Masu bukatar taimakon abinci na kara karuwa

A duk tsawon lokacin matsalar tattalin arziki da kasashen duniya suka sami kansu a ciki kasar Netherlands, ba kamar sauran kasashe ba al'amuranta sun kasance cikin nasara.

Sai dai kuma a yanzu gwamnatin Fraiminista Mark Rutte ta wargaje saboda sabanin da aka samu akan matakan rage kasafin kudi, baya ga wannan ma akwai kuma karin alamun matsalolin tattalin arzikin.

wata alama ita ce ta karin bukatar samun taimakon abinci, kamar yadda ake iya gani a wani sako na wani titi mai yawan jama'a da ababan hawa a Amsterdam, inda ake iya ganin jerin layin masu neman taimakon abincin.

A kasan benen cibiyar bada taimakon abincin masu aikin sa kai na kai kawo su na ta aikin ware taimakon kayayyakin abinci kafin mabukata su fara tururuwa don karba.

Wannan dai daya ce daga cikin cibiyoyi biyar na bada taimakon abinci a birnin.

A 'yan watannin da suka gabata an sami karin mutanen da ke bukatar taimakon abincin yadda ba a taba samu ba a baya. Wani daga cikin ma'aikatan cibiyoyin bada taimakon abincin na Amsterdam Piet van Diepen, yace kimanin iyalai 1,300 ne ke zuwa neman tallafin a ko wana mako, kuma yawansu na cigaba da karuwa da a yanzu ma lamarin ya yi kamari.

Yace muna ganin tasirin matsalar tattalin arzikin a zahiri.

Mutanen da suke zuwa neman tallafin sun rasa ayyukansu gashi ba su da kudi ga dinbin bashi a kansu sannan kuma gwamnati na rage taimakon da ta ke baiwa jama'a, a don haka dole ne mutane su zo nan.

Wata 'yar kasar ta Netherlands, Petra, tace kudin da ake biyanta ba sa iya biyan bukatunta na abinci.

Mutanen da suke zuwa karbar taimakon abincin na karuwa da kashi goma cikin dari a kowana wata tun daga watan Disamba.

A yanzu sama da mutane 60,000 ne a fadin kasar ta Netherlands, suka dogara da wuraren bada taimakon abincin don samunn abinda zasu ci.

'Fatara a boye'

Petra na daya daga cikin mutanen da suka fara zuwa domin samun tallafin abincin, tana dauke da wasu jakunkunanta biyu ,nan da nan ta shiga duba irin kayan abincin da aka tanadar ta debi wanda take bukata.

Ta ce wannan makon al'amarin sai hamdala.

Ga kayan lambu da yawa da biskit da 'ya'yan itatuwa ga ganyayyaki da za a hada da taliya , kai abin alasanbarka, wadansu lokutan ganyen salad ne kawai.

Ita dai Petra shekaru uku kenan tana zuwa wannan wuri.

Yayinda ta ke dibar kayan abincin ta na zubawa a jakunkunanta ,sai ta ke bayyana cewa kudin da ake bata a kowana mako euro 50 kwatankwacin fam 40 ba zai isa ciyadda iyalinta ba.

Tace idan da babu wuraren bada taimakon abincin da sai dai ta shiga wani mummunan yanayi, da zai iya kai ta ga sata saboda batada abin da zata ci.

Tace akwai fatara sosai a Holland amma a boye ta ke , ba wanda ya sani.

Batun yunwa ba abu ne da za ka danganta shi da daya daga cikin kasashen turai masu karfin tattalin arziki ba.

Amma matakan tsuke bakin aljihu da shugabanni a koli ke dauka na matukar shafar rayuwar jama'a.

Image caption Wasu mata a gidan cin abinci

Tattalin arzikin kasar yanzu yana dakushewa.

Matsalar rashin aikin yi ta kai kashi shida cikin dari, matakin da bata taba kaiwa ba cikin shekaru 6.

Daya daga cikin kowana iyalai 6 na fafutukar yadda zai biya kudin cefanansa na sati.

Sai dai a wurin shaye -shaye da cin kayan kwalan da makulashe na Basis dake birnin Amsterdam wanda ke da 'yar tazara daga wurin bada taimakon abincin, masu cin abincin dare wadanda ke kokarin ganin yanayin matsin tattalin arzikin bai jirkita musu yanayin rayuwar da suka saba ba na ta tururuwa zuwa wurin.

A nan zaka iaya zuwa da abincinka daga gida ma'aikatan wurin zasu dumama maka abincin a kyauta abinda zaka biya shi ne abinda zaka sha kawai.

Michiel Zwart shi ne mai gidan shaye shayen wanda yake cewa abune da ke cin kudi sosai ace ka rinka cin abinci koda yaushe a gidajen abinci amma a nan abu ne mai ban sha'awa domin ba zaka kashe kudi mai yawa ba.

ya ce wannan salad din da ka ke gani a nan da euro biyar zaka saye shi amma idan ka tsallaka titi can kusan euro 10 zuwa 15 zaka saye shi.

Gidan shaye-shayen da kwalan da makulashen na Basis,koda ike bai yi nufin ya ci ribar matsalar tattalin arzikin da ake ciki ba ama mai wurin ya lura da samun karuwar mutanen da suke zuwa wurin wadanda ke neman rahusa.

Mr zwart yace mutane ba su da isassun kudaden da zasu rinka zuwa gidajen cin abinci suna cin abinci yanzu, a don haka muka saukaka musu muka tsara yadda za su cigaba da fitowa daga gidajensu su gana da abokanansu ba tare da sun kashe wasu kudade masu yawa ba wajen sayen abinci.

Yace a nan munada mutanen da suke zuwa da katuwar tukunyarsu ta miya daga gida, su dumama abincinsu suci su hole tsawon dare a farashi mai sauki.

Girki domin rayuwa:

A wani sashe na birnin na Amsterdam, Denise Dulcic 'yar shekara 32, ta dukufa tana girki da wani risho.

Da aka tambaye ta gameda cin abinci a otal sai tayi dariya tace, cin abinci a waje? Bar wannan magana!

Ita dai Denise tana girka fiye da abincin da zai ishe ta sai ta saida sauran da ta rage .

Ta rasa aikinta ne lokacin da gwamnatin kasar ta Holland, ta rage yawan kudin da take warewa fannin ilimi na musamman saboda tana koyarda yara ilimin sanin halayya kuma tun sannan bata sake samun wani aikin ba.

Tace dolece tasa take yin wannan dabara ta yin girki domin taci ta kuma saida saboda babu wani aiki na sosai da ta samu wanda zatayi.

Ta ce tanada kwarewar da ta kamata amma babu aiki. Yanzu dai Denise ta na gudanar da rayuwarta ce ta sabuwar dabarar sana'ar dafa abincin da zata ci ta kuma saida ragowar hadi da 'yar sana'ar data fara jarrabawa ta bada shawara ga marassa lafiyar da ta jibanci halayya.

Tace abune mai wuyar gaske ta rayu da sana'ar girki kadai.

Tace biyan kudin hayar gida kadai abune mai wuya saboda kudin yayi yawa

Ta ce girki abin nishadinta ne amma yanzu tana yin sa ne don dole domin ta rayu.

Yayinda 'yan siyasar Holland, suke dambarwar zaftare karin euro biliyan 9 daga kasafin kudin kasar mutanen da suke neman kaucewa fadawa tsaka mai wuya sanadiyyar matakan tsuke bakin aljihun na cigaba da karuwa