China ta nemi kasashen Sudan su zauna lafiya

Yaki a yankin Sudan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yaki a yankin Sudan

China ta yi kira ga kasashen Sudan da Sudan ta Kudu da su kai zuciya nesa a rikicin da suke gwabzawa, wanda ake fargabar zai iya mayar da kasashen yaki gadan gadan.

A halin da ake ciki shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir na wata ziyarar aiki a China, inda yayin wata ganawa da shugaba Hu Jintao, ya zargi Sudan da kaddamar da yaki a kan kasarsa.

China dai ta dade tana huldar kut da kut da kasar Sudan.

Yayin da jami'an Sudan ta Kudu ke zargin jiragen yakin Sudan da sake kai hare hare a cikin kasarsu, su kuma hukumomin Sudan na cewa zasu dauki dukan matakan da zasu iya, wajen yaki da fasakwaurin abinci zuwa cikin kasar Sudan ta Kudu.

Karin bayani