Ana son kai a fannin tattalin arzikin duniya, in ji BBC

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Tambarin BBC

Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa tun fiye da shekaru uku jama'a a sassan duniya da dama suke korafi game da yadda ake fifita wasu ta bangaren harkokin tattalin arziki.

Ra'ayoyin da kamfanin GlobeScan ya tattaro, a madadin BBC sun nuna cewa mafi rinjayen mutane a kasashe goma sha bakwai cikin ashirin da biyu sun yi imanin cewa kalilan ne ke amfana da ribar da ake samu a hada-hadar tattalin arziki a kasashen su.

Lamarin ya fi fitowa karara a kasar Spain wadda ta fuskanci matsalolin tattalin arziki.

An kuma gano hakan a kasashen India da Amurka.

Karin bayani