An kashe mutane biyar a Pilato

Jami'an tsaro a Nijeriya
Image caption Jami'an tsaro a Nijeriya

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa wasu 'yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba, sun kai hari a karamar hukumar Riyom jiya da dare inda suka kashe mutane biyar.

Rundunar tsaro ta kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato ta tabbatar da mutuwar mutanen, amma ta ce kawo yanzu jami'an tsaro ba su kama kowa ba dangane da kai harin.

Harin 'yan bindigar a karamar hukumar Riyom ya zo ne a kusan lokaci guda da aukuwar fashewar wani abu da ake kyautata zaton bom ne a Jos babban birnin jihar ta Filato, inda hukumomin tsaro suka ce fashewar ta yi sanadiyyar jikkata mutane tara.

Fashewar dai ta auku ne a wajen wani gidan kallon talabijin dake unguwar Tudun Wada, kusa da inda a kwanakin baya aka samu irin wannan fashewar.

Karin bayani