Murdoch ya bayyana a gaban kwamitin binciken kafofin watsa labarai

Rupert Murdoch
Image caption Rupert Murdoch

Hamshakin Attajirin nan da ya mallaki kafafen yada labarai, Rupert Murdoch, ya bayyana wa hukumar bincike ta Birtaniya a kan ka'idojin aikin jarida cewar bai taba neman wata alfarma a wajen wani Pirayi Minista ba.

Mista Murdoch ya ce yana son ya kawo karshen, karerayin da ake cewar yayi amfani da karfin daya daga cikin jaridunsa a Birtaniya wato The Sun, don samun tagomashi daga gwamnati.

Ya ce, "ban taba barin bukatar kasuwanci na ya shiga cikin harkokin zabe ba. Idan kuma ba haka, to ba ni misali."

Mista Murdoch ya kara da cewar idan da burinsa shi ne na cin ribar kasuwanci, to a kodayaushe da zai dinga goyon bayan jamiyyar Conservative ta masu ra'ayin rikau ne.

Karin bayani