Bama-bamai sun fashe a Najeriya

Bam ya tashi a ofishin jaridar This Day
Image caption Wannan ne karon farko da aka kai hari kan ofishin wata jarida a Najeriya

A kalla mutane shidda sun mutu bayan wasu bamabamai sun fashe a wasu gidajen jaridu a garuruwan Abuja da kuma Kaduna a Najeriya.

Bam din na Abuja ya tashi ne a cikin mota a ofishin jaridar This Day.

Jami'a sun ce akalla mutane ukku ne suka mutu a lamarin na Abuja wanda aka ce harin kunar bakin wake ne

Wasu rahotannin kuma sun ce dan kunar bakin wake ya tayar bam a wani gini da ma'aikatan jaridar This Day da The Moment da Daily Sun suke zama a garin Kaduna, kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka ce.

Bam din ya haifar da mummunar fashewar, kamar yadda wani jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP.

Akalla mutane uku ne suka mutu a fashewar da ta afku a ofishin This Day, a cewar wani jami'in Red Cross da ya yi magana da Reuters.

'Abin kunya ne'

Fashewar bam din na Abuja ta faru ne da misalin karfe 11:30 agogon Najeriya.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaro sun killace wurin da lamarin ya faru.

"Silin ginin ya rufto kan kwamfiyutocinmu sakamakon fashewar," kamar yadda wani ma'aikaci a kusa da ginin ya shaida wa BBC.

A wata sanarwa da aka fitar, shugaba Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa "abin kunya ne, da rashin sanin ya kamata wanda kuma bai dace ba."

Gwamnati za ta ci gaba da "kokarinta na tabbatar da damar fadar albarkacin baki wanda tsarin mulki ya bayar da kuma 'yancin 'yan jarida baki daya,"a cewar sanarwar. "Miyagun da ke kokarin sanya tsoro tsakanin zukatan 'yan Najeriya da ma 'yan kasashen waje ba za su yi nasara ba."

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a kasar.

An zargi kungiyar da kashe mutane akalla 440 a bana kawai, kamar yadda wani kiyasi na kamfanin dillancin labarai na AP ya nuna.

A baya kungiyar ta kai hare-haren kunar bakin wake kan ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja wanda ya kashe mutane akalla 25.

A ranar 18 ga watan Afrilu ofishin jakadancin Amurka ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar kai hari a Abuja, kan wasu wurare da suka hada da otel-otel da 'yan kasashen waje ke ziyarta.

Karin bayani