Fryministan Pakistan zai daukaka kara

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yousuf Raza Gilani

Lauyoyin Fryministan Pakistan, Yousuf Raza Gilani sun ce, zai daukaka kara dangane hukuncin da kotun koli ta yanke masa bisa laifin raina kotu.

Kotun kolin kasar dai ta samu Yusuf Raza Gilani ne da laifin yin burus da umarnin da da kotun ta ba shi akan ya rubuta wasika zuwa ga hukumomin Switzerland domin a sake soma tuhumar aikata cin hanci da rashawa da ake yiwa shugaban Pakistan din, Asif Ali Zardari.

Sai dai kotun ta zartar wa Mr Gilanin da hukuncin da ba ta fayyace ba, ta kyale shi ya ci gaba da zama kan mukaminsa zuwa wani lokaci.

A yanzu dai ba za a iya tantance wa ba ko wannan hukunci zai sanya a sauke shi daga mukaminsa a nan gaba.

Karin bayani