Mai fafutuka a China ya tsere

Daya daga cikin masu fafutikar da suka fi fice a China, Chen Guangchen, ya tsere daga daurin talalar da ake masa a gabashin kasar, kuma ya fitar da wani fefen bidiyo yana rokon gwamnatin kasar kai tsaye.

Magoya bayansa sun ce mai fafutukar, wanda makaho ne na nan lafiya a wani waje a birnin Beijing bayan da aka sato shi daga kauyensu dake lardin Shandong a gabashin kasar.

A faifai bidiyon da ya sa a internet, Mr Chen ya roki praminista, Wen Jiabao da ya kare lafiyar iyalinsa, yana mai cewa, tilas ne a gurfanar da jami'an garinsu akan mummunan harin da suka kai masa da matarsa.

Karin bayani