Adadin marasa aiki ya karu a Spain

Adadin marasa aiki ya karu a Spain Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyoyin kwadago na adawa da matakan da gwamnati ke dauka

Hukumar kula da kididdiga ta Spain ta ce adadin marasa aikin yi ya karu a kasar zuwa sama da miliyan biyar da rabi (5,639,500) a karshen watan Maris da ya gabata.

Wadannan alkaluma sun zo ne sa'o'i kadan bayan da hukumar kula da darajar kasashe wurin karba da biyan bashi ta Standard & Poor's ta rage darajar kasar ta Spain.

Ana saran alkaluman da hukumomi za su fitar a ranar Litinin za su tabbatar da cewa Spain ta sake komawa cikin mummunar matsalar tattalin arziki.

A farkon makon nan ne babban bankin kasar ya ce tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma-baya da kashi 0.4 cikin dari a watanni ukun farko na bana, bayan ya ja baya da kashi 0.3 a watanni ukun karshe na bara.

Sauran alkaluman da aka fitar ranar Juma'a sun nuna cewa harkokin saye-da-sayarwa na kasar sun yi kasa da kashi 3.7 a watan Maris.

Watanni 21 kenan a jere harkokin cinikayya na fuskantar koma-baya a kasar Spain.

'Babbar matsala'

A watanni ukun farko na bana, mutane 365,900 ne suka rasa ayyukansu a kasar.

Kasar ta Spain ita ce ke da adadi mafi girma na marasa ayyukan yi a Tarayyar Turai, kuma ana saran adadin ya ci gaba da karuwa nan gaba a bana.

Adadin ya ci gaba da karuwa tun daga watan Afrilun 2007, lokacin da ya tsaya a kashi 7.9 cikin dari.

"Wadannan alkaluma ababen damuwa ne ga kowa-da-kowa da kuma gwamnati... Spain na cikin babbar matsala," a cewar ministan harkokin waje Jose Manuel Garcia-Margallo.

Karin bayani