Kungiyar 'yan jarida ta yi Alla-wadai da harin da aka kai a Najeriya

Image caption Gidan jaridar Thisday

Kungiyar 'yan jaridu ta Najeriya ta bayyana damuwar ta game da harin da kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta kai ranar Alhamis a kamfanin jaridar Thisday.

Kungiyar ta ce za ta gudanar da taron gaggawa don tabbatar da cikakken tsaro a kamfanonin jaridun kasar.

Shugaban kungiyar, Malam Garba Muhammad, ya ce bai kamata kungiyoyin da ke tayar da kayar-baya su rika daukar 'yan jarida a matsayin makiyansu ba.

Ya kara da cewa 'yan jarida na gudanar da ayyukansu ba tare da nuna son rai ba.

Hare-haren bama-bamai da aka kai a ofishin kamfanin na Thisday a Abuja da Kaduna ya kai ga asarar rayuka da barnar dukiya.

Karin bayani