PDP ce ta haifar da Boko Haram, in ji Azazi

Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara a harkokin tsaro, Janar Andrew Azazi, ya dora alhakin matsalar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a arewacin kasar a kan jam'iyyar PDP.

Mr Azazi ya ce tsarin jam'iyyar na fifita wani dan takara ta hanyar nadi maimakon zabe na daga illolin da suka haddasa matsalar.

Ya ce wannan rashin adalci ne ya sanya matsaloli irin na Boko Haram suka ta'azzara, yana mai cewa akwai siyasa a cikin lamarin.

Ya kara da cewa ko da an kame shugabannin kungiyar Boko Haram din gaba daya, ba za a kawo karshen rikicin ba saboda ba addini, ko talauci ne kawai suka sanya matsalar ba.

Mr Azazi ya ce ya kamata a duba wasu hanyoyi don magance matsalar, ba kawai amfani da karfin soja ba.

Karin bayani