An yi zanga zanga mafi girma a Malaysia

Zanga zanga a Malaysia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga zanga a Malaysia

A Malaysia, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma mesar ruwa, a lokacin daya daga cikin zanga zanga mafi girma da aka gudanar a kasar a cikin shekaru da dama, don neman a yi wa tsarin zabe gyaran fuska.

Jami'an tsaron sun dau matakin ne, bayan da wasu daga cikin masu zanga zangar suka yi kokari kutsawa cikin shingayen da aka kakkafa, a tsakiyar Kuala Lumpur, babban birnin kasar ta Malaysia.

Masu zanga zangar na son a yiwa rajistar masu zabe kwaskwarima, da kuma sauran tsare-tsare na zabe, wadanda suka ce sun fifita jam'iyya mai mulki.

Karin bayani