An kashe ma'aikacin Red Cross a Pakistan

'Yan kungiyar Taliban Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan kungiyar Taliban

Kungiyar agajin Red Cross a Pakistan ta ce, mutanen da suka yi garkuwa da wani ma'aikacinta, dan kasar Birtaniya, sun hallaka shi a lardin Balochistan na kudu maso yammacin kasar.

A watan Janairu ne aka sace Dokta Khalil Rasjed Dale, daga birnin Quetta.

Jami'an 'yan sanda sun ce, yau da safe ne aka gano gawarshi, an fille masa kai, tare da wata wasikar da ke cewa, 'yan Taliban na Pakistan ne suka kashe shi.

Kisan nasa shine na baya baya a lardin na Balochistan, inda ake zaman kara zube, sakamakon gwagwarmayar da wasu ke yi ta neman ballewa daga Pakistan, da kuma tada kayar bayan 'yan Taliban.

Karin bayani