Za a sake yiwa al-Khawaja sharia a Bahrain

Abdul -Hadi al- Khawaja Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Abdul -Hadi al- Khawaja

Wata kotu a Bahrain ta bayar da umurnin a sake shari'ar mai yajin cin abincin nan wanda aka daure saboda jagorantar zanga zangar neman kafa mulkin Demokuradiya a Bahrain.

Wata kotun soji ta samu Abdul-Hadi al-Khawaja da wasu masu fafutikar 20 da laifi a bara.

A halin yanzu wata kotun farar hula ce za ta sake bin ba'asin shari'ar tasu.Abdul-Hadi Khawaja zai ci gaba da zama a gidan yari.

Matarsa ta ce hukumomin Bahrain na neman yin wani sassauci marar tasiri ne don jan kafa, tana mai cewa ba za a samu wani bambanci tsakanin alkalan kotun farar hular da kuma na kotun sojin ba.