Bom ya yi kisa a jihar Taraban Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu yayinda wasu da dama suka samu raunuka a wani harin bom da aka kai yau a garin Jalingo babban birnin jihar Taraba dake arewacin Najeriya.

Wani jami'in jinya a cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Jalingo ya shaida wa BBC cewa shi da kansa ya kirga gawa uku yayinda da dama suka samu raunuka.

Sai dai wasu majiyoyin na cewa mutanen da suka rasa rayukansu sun kai akalla bakwai.

Harin na zuwa ne kwana daya bayan hare-haren da aka kai wa wasu masu ibadar kiristoci a jihohin Kano da Borno wadanda suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 21.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da hare-haren da ya kira na ta'addanci, sannan ya ce hare-haren da aka kai a baya-bayan nan a kan gidajen jaridu da kuma cibiyoyin bada ilmi mai zurfi, ya nuna wadanda suke kai su suna son su rusa zaman lafiyar da ake da shi ne a Najeriya.

I zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai hare-haren, sai dai masu sharhi a kan al'amura na ganin sun yi kama da hare-haren da kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunah Lidda'ati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram ke kaiwa.

Tattaunawa

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriyar ta sake yin kira ga 'ya'yan kungiyar nan ta jama'atu Ahlus- sunna lidda'awati wal- jihad da aka fi sani da Boko Haram, da su fito a tattauna da su domin kawo karshen hare-haren da kungiyar take kaiwa.

Kiran na gwamnatin Najeriyar dai yazo ne kwanaki kalilan, bayan wasu hare-hare da aka kaddamar a kasar.

A wata ziyara da ya kai Jihar Gombe, mataimakin shugaban Najeriya, Architect Namadi Sambo ya yi kira ga kungiyar da ta fito a tattauna da ita domin samar da zaman lafiya a kasar.

"Ina kira ga wadannan mutane su fito a zauna da su domin a samu maslaha, ko shekaru hamsin aka yi ana yaki, dolene a zauna a teburin sulhu domin a samu maslaha." In ji Namadi Sambo.

Gwamnatin kasar dai ta nanata cewa za tayi iyakacin kokarinta domin tabbatar da tsaro a kasar inda mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo ya nemi al'ummar kasar da su taimakawa gwamnati kasar wajen tabbatar da tsaro a kasar.

"Zamu ci gaba da kokari, ganin cewa ko wane dan Najeriya a fadin kasar nan a ko ina ya samu isashen tsaron lafiya da kuma dukiyoyinsu.

"Muna kira ga 'yan Najeriya su bada tasu gudunmuwar wajen taimakawa gwamnati magance matsalolin tsaron dake addabar gwamnatin kasar." In ji Namadi Sambo.

To sai dai kuma wasu na ganin cewar Gwamnatin Najeriyar bada gaske take ba, suna masu cewar ai gwamantin ta soma wannan tattaunawar da kungiyar a baya, daga baya kuma alamu suka bayyana cewa bada gaske gwamnatin take ba, don haka ma tattaunawar ta wargaje.