An kai hare haren bam a birnin Idlib na Syria

Ta'adin  hare-haren bam a Idlib Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ta'adin hare-haren bam a Idlib

Mutane akalla 9 ne aka kashe kuma wasu kusan dari daya ne suka samu raunuka a fashewar wani abu a birnin Idlib na Syria.

Rahotanni sun ce wasu manyan bama bamai 3 sun tashi, biyu daga cikinsu sun hari gine ginen hukumar tsaro.

Masu fafutika na yan adawar Syria sun ce yawan mutanen da suka mutu sun fi 20, hade da jami'an tsaro da fararen hula.

Kamfanin dillancin labarai na Syriar ( SANA ) ya ce, tashin bam din aikin wasu yan kunar bakin wake ne.

Gidan TV na Syria ya dora alhakin hare haren a kan wasu yan kunar bakin wake da bam.

Hotunan TV sun nuna barna mai dama ga gine gine da yawa, da mutanen da suka tagayyara da kuma jinin da ya malala na wadanda lamarin ya shafa.