An kashe mutane a rikicin jihar Filato

Jami'an tsaro a birnin Jos
Bayanan hoto,

Jami'an tsaro na sunturi a birnin Jos na jihar Filato

Rahotanni sun ce akalla mutane shida aka kashe tare da kona gidaje da rugage da dama a wani rikici da ya barke a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato da ke Najeriya.

An fara tashin hankalin ne tun ranar Litinin, kuma ya ci gaba da gudana har wayewar garin Talata, amma dai kawo yanzu hukumomin tsaro sun girke Karin dakaru a yankin.

Wakilin BBC Ishaq Khalid a birnin Jos ya ce tashin hankalin da aka soma ya fi shafar kauyukan Rim da Falwaya da Bangal, inda aka kona gidaje da rugage da dama kana aka samu hasarar rayukan bil Adama sannan kuma mutane da dama suka tsere daga gidajensu.

Tashin hankalin dai tsakanin Fulani ne da kabilar Berom kuma dukkan bangarorin biyu na zargin juna da fara haddasa rikicin.

Mista Francis Jamang shugaban kungiyar matasan kabilar Berom na Kasa, ya shaida wa BBC cewa Fulani ne suka kai musu hari.

'Su kai zuciya nesa'

"Fulani na zargin Berom ne da far masu tare da daurin gindi na jami'an tsaro inda suka kona masu rugage da dama", kamar yadda shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a karamar hukumar Riyom, Alhaji Mato ya shaida wa BBC.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato Samuel Dabai, ya tabbatar da kona gidaje da dama amma yace kawo yanzu basu kai ga tabbatar da hasarar rayuka ba.

Sai dai kuma wasu majiyoyi a yankin na Riyom sun tabbatarwa da BBC mutuwar mutane shida.

"Wajibi ne Fulani da Berom din su kai zuciya nesa sannan su rungumi hanyar zaman lafiya yayin da aka tura Karin jami'an tsaro zuwa yankin", a cewar Samuel Dabai, kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar.

Bisa dukkan alamu dai tashe-tashen hankulan da jihar Filato ta dade tana fama da su wadanda suka dan tsagaita na watanni, yanzu sun sake kunno kai.

A 'yan kwanakin nan, alkaluma sun nuna cewa mutane kimanin goma sha biyar ne suka rasa rayukansu a kashe-kashe daban-daban a jihar.