Amurka ta bada hujjar amfani da jirage masu sarrafa kansu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Amurka, Barack Obama

Babban mai baiwa Shugaba Obama Shawara a kan ta'adanci, John Brenan ya bada hujojin da ya sa Amurka ke amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kisan manyan jami'an kungiyar Al-Qaida.

A wani jawabi da Mista Brenan ya yi a Washington ya ce hare-haren da kasar ke yi da jiragen yaki ya taimakawa gaya wajen yaki da kungiyar Al'qaida a Afghanistan da Pakistan da kuma Yemen.

Ba wannan bane karon farko da gwamnatin shugaba Obama ke amince tana amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare ba.

A watan Junairun daya gabata ma, Shugaban Obama da kansa ya amince da hakan a wata hira a shafin Internet.

Amma John Brennan ya bada karin haske ne da kuma dalilin da ya sa Amurka ke amfani da salon yakin da ake cece kuce a kansa.

Ya ce Shugaban kasa ya umarce shi da fayyace 'yan Amurka yadda batun yake, inda ya kara da ce matakin ba laifi ba ne, kuma ba su zarta ka'ida ba kana kuma dabara ce da ta dace.

Babban mashawarcin shugaba Obama kan yaki da ayyukan ta'addanci, John Brenan ya ce ana daukar matakan taka-tsantsan sosai domin kauce kisan fararen hula, amma ya amsa cewa a wasu lokuttan ana kashe fararen hular.

Ya ce a karon farko kungiyar Al-Qaida ta fara samu koma baya tun da Amurka ta fara kaddamar da yaki a kan 'ya yan kungiyar.