Za mu ci gaba da kaiwa kafafen yada labarai hari - Boko Haram

Boko Haram Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Boko Haram na fafutukar kafa tsarin shari'ar Musulunci a Najeriya

Kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram a Najeriya,, ta yi barazanar ci gaba da kaiwa wasu manyan kafafen yada labarai da ma'aikatansu hari a kasar.

Daga cikin kafafen yada labaran da kungiyar ta ce za ta kaiwa hari ba tare da wani gargadi ba, sun hada da gidan jaridun Punch, Daily Sun, Vanguard da Tribune.

Wannan rukuni kuma kamar yadda mai bayani a faifan bidiyon You Tube ya ce, sun hada da gidan radiyo na sashen Hausa na Muryar Amurka, VOA, saboda abun da kungiyar ta ce shirye-shriyen da suke ke yi na kira ga jama'a su tona asirin 'yan kungiyar.

Kungiyar ta jera dalilan da ya sa ta kai hari kan ofishin jaridar Thisday, wadanda suka hada da cin zarafin Annabi Muhammad (SAW) a wani rahoto da jaridar ta wallafa a watan Nuwamba na shekara ta 2002.

Da kuma bayyana cewar kungiyar na da hannu a garkuwa da kisan da aka yiwa wasu turawa biyu a Sokoto, duk kuwa da cewar kungiyar ta bayyana cewar babu hannunta a wannan garkuwa.

Yadda aka kai harin

Haka nan kuma kungiyar ta ce, gidan jaridar ya ci gaba da daukar bahasin gwamnati na cewar an kama Abul-Qaqa ne, a madadin Abu Darda, kamar yadda kungiyar ta sha bayyana.

Hoton bidiyon ya nuna yadda aka kai harin a cikin wata mota kirar jeep, da kuma hoton wanda kungiyar ta ce shi ne ya kai harin, da ma lokacin da ya tuka motar cikin harabar kamfanin Thisday kuma nan take bom din ya tashi.

Kungiyar ta kasafta kafofin yada labarai zuwa gida ukku, inda ta ce gidan Jaridar Thisday shi ne kan gaba, saboda dalilan da ta bayyana.

Bayan haka, kungiyar ta ce akwai wasu kafafen yada labarai da ke dab da fadawa rukunin wadanda za su kai wa hari matukar ba su yi hattara ba.

Kafofin yada labaran sun hadar da, gidajen jaridu na Leadership, Daily Trust da kuma sashen Hausa na gidan Radiyon Faransa, watau RFI.

Sakon ya kuma kara da cewa matukar gwamnati ba ta daina kame matan 'yan kungiayar da yara ba, tare kuma da rusa musu gidaje, to za su ci gaba da rusa gine-ginen gwamnati.

Boko Haram sun kuma dauki alhakin harin da aka kai a jami'ar Gombe da kuma Bayero University da ke Kano, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Karin bayani