Jami'an tsaro sun kashe mutum daya a Kano

ig Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Speto Janar na 'yan sandan Najeriya, Muhammed Abubakar

Rundunar tsaron hadin gwiwa a jihar Kano dake arewacin Najeriya ta ce jami'anta sun kashe mutum daya, a wata musayar wuta da aka yi gab da asubahin ranar Talata a samaman data kai a unguwar Bubbugaje dake yankin Sharada.

Haka kuma rundunar tace ta samu mata uku a gidan da abubuwan fashewa da bindiga da albarusai.

Wannan sumame dai na zuwane a daidai lokacin da wasu jami'an tsaro ke kokawa da rashin kula da walwalarsu duk da hadarin da suke ciki.

Jami'an tsaro a Kanon, sun ce sun kai samamen ne bisa bayanan cewar gidan, maboya ce ta wasu 'yan gwagwarmaya, bayan hare haren da aka kai ranar Lahadi a Jami'ar Bayero, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla sha shidda.

Jami'an tsaron sun ce sun gano bamabamai hadin gida masu yawa a cikin gidan.

Tun a cikin dare ne mazauna anguwar da lamarin ya faru ke cewa sun yi ta jin karar harbe harben bindiga da kuma fashewar nakiyoyi.

Karin bayani